1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi kira ga bangarori biyu na Libiya

Binta Aliyu Zurmi
October 12, 2020

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kasar Libiya, Stephanie Williams ta yi kira ga bangarorin biyu da ba sa ga maciji da su saka son kasa a gabansu maimakon burin siyasa gabannin zaman watan gobe.

https://p.dw.com/p/3jpJK
Libyen Truppen von General Haftar zurückgedrängt
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Stephanie Williams ta yi wannan kiran ne domin kawo karshen dadadden rikicin kasar da ya janyo asarar rayuka da dama.

Kasar Tunisiya ce za ta karbi bakuncin wannan muhimmin zama tsakanin madugun adawa Khalifa Haftar da kuma bangaren gwamnatin Fayez al-Siraj wanda MDD ta aminta da shi.

Ministan harkokin wajen Tunisiya Othman Jerandi na fatan wannan tattaunawar za ta lalubo da mafita a siyasance ga bangarorin biyu.