MDD na fargabar rincabewar rikicin Yemen da Gabas ta Tsakiya
January 13, 2024Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta kan cewa rikicin da aka fara fuskanta a Yemen game da hare-haren jiragen ruwa a Kogin Baharmaliya, ka iya zama silar gaza kawo karshen rikicin kasar da aka jima ana fama.
Karin bayani:Bahar Maliya: Takaddamar Amurka da Houthi
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen Hans Grundberg ne ya yi wanna jawabi, yana mai cewar wajibi ne a kare fararen hular kasar Yemen, tare da kokarin yayyafawa wutar rikicin ruwa don samun dawwamammen zaman lafiya a yankin.
karin bayani:Iran na yunkurin kawo karshen yakin Yemen
A cikin makon nan da muke bankwana da shi ne dai Amurka da kwayenta suka kaddamar da hare-hare da dama kan kasar, a kokarinsu na farwa 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, da ke ci gaba da kai hari kan jiragen ruwan da ke bi ta Baharmaliya, a matsayin martanin yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.