1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Mayar da 'yan Nijar gida daga Libiya

November 5, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an yi amfani da jiragen aikin jin kai wajen mayar da wasu ‘yan Nijar 172 masu neman mafaka  zuwa birnin Yamai daga kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/42eEo
Flüchtlinge aus Kongo
Hoto: imago/Independent Photo Agency/M. Amoruso

Cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Tripoli, hukumar ta ce da yawa daga cikin wadanda aka kwashe na cikin mummunan yanayi sakamakon fataucinsu da aka yi, yayin da wasu kuma suka sha fama da tashin hankali a Libiya.

Tun dai bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011 ne Libya ta zama cibiya ga dubun dubatar bakin haure na kasashen Afirka da ke neman shiga Turai ta tekun Bahrhum. Sai dai sojojin da ke kare ruwan Libiya na amfani da karfi wajen tsare bakin hauren da suka kamo, lamarin da kungiyoyi masu zaman kansu da Majalisar Dinkin Duniya suka yi tir da shi.

A karshen watan Oktoba ne Libiya ta ba da izinin dawo da zirga-zirgar jiragen sama na jin kai, wanda aka dakatar kusan shekara guda da ta gabata, lamarin da hukumar ta yi maraba da shi tana mai cewa  wadannan jiragen za su bada damar ceto rayukan daruruwan bakin haure da 'yan gudun hijira.