1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD Hakkin dan Adam

December 9, 2005

Duk wata kasa dai na da hakkin kare al'ummanta daga hare-haren ketare ko kuma na cikin gida. Amma hakan na hujjanta yin watsi da ka'idojin kare hakkin dan Adam ke nan ?

https://p.dw.com/p/Bu3V
Alamar kungiyar CIA
Alamar kungiyar CIAHoto: Getty Images /G. Gershoff

A halin yanzu dai, batun da aka fi yin muhawara a kansa a cibiyoyin mulki da dama na kasashen yamma da Amirka shi ne na warware tambayar nan ta dalilan da ke hujjanta gallazawa wa fursunoni da ake zargin jami’an tsaron Amirka da aikatawa. Wai shin dokar nan ta kasa da kasa da ta haramta azabtad da fursunonin da aka tsare, ko’ina kuma suke a duniya, ba ta aiki ke nan a lokacin yaki, ko inda aka kafa dokar ta baci, ko kuma inda aka ga cewa akwai kasadar kai harin kunan bakin wake na `yan ta’adda ?

Wannan dai ita ce tambayar da ta fi jan hankullan masu fada a ji a fagen siyasar nahiyar Tuari, bayan buga rahotannin da aka yi, wadanda ke zargin jami’an tsaron Amirka da gallaza wa fursunonin da suke tsare da su, a sansanonin sirrin da suka kafa a kasashen gabashin Turai da wasu yankuna na duniya.

Tun 1948 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta haramta azabtad da fursunoni, a cikin wasu kudurorin da ta zartar, wadanda kuma har ila yau suka zamo wajibi ga duk kasashe mambobinta. Ko wane irin take hakki na dan Adam dai wato ya zo daidai da rashin girmama martabarsa. Azabtad da wanda aka tsare kuma, saboda dalilai daban-daban, wato wuce gona da iri ne a wannan huskar. Babu wani dalilin da ke hujjanta azabtad da wadanda ake tuhuma da aikata laififfuka, don samo karin bayani a lokacin da ake yi musu tambayoyi, ko ta hanyar wulakantad da su, ko ta sanya su cikin wani hali da bai da ce da darajar da halitta kamar dan Adam ya cancanci ya samu ba.

Sakamakon da gallaza wa wadanda ake tuhuma ke janyowa na da yawa. Su da kansu masu azabtarwar ma, na zamowa wasu irin halittu maras imani sannu a hankali. Kazalika kuma duk wata kasar da ke goyon bayan wannan mummunar dabi’ar, ko kuma ba da umarnin a aiwatad da ita, to ita ma kwarjininta na dusashewa a idanun duniya. Ba za a iya dai samun cudanya tsakanin al’ummomin wannan duniyar tamu ba, sai an cim ma wani daidaito na bai daya na daraja martabar dan Adam, wanda kuma kowa zai amince da shi.

A yunkurin yakan ta’addanci dai, bai kamata a ce wata kasa ta yi watsi da ka’idojin kare hakkin dan Adam ba. Duk kasar da za ta yi hakan kuwa, babu shakka, za ta huskanci rashin amincewar al’ummanta da kuma na gamayyar kasa da kasa.

Wadannan ka’idojin kuwa, sun rataya ne a wuyar duk kasashen duniya har da ma Amirka da nahiyar Turai. Musamman ma dai, su kasashen yamman ne ya kamata su shiga sahun gaba, wajen nuna misalli a zahiri, a fafutukar daraja martabar dan Adam da kuma kare hakkinsa. Sabili da haka, yanzu da aka bayyana labaran gallaza wa fursunoni da jami’an kungiyar leken asirin Amirka, wato CIA ke yi ko kuma suka yi, a wasu sansanonin sirrin da suka kafa, to kamata ya yi, a dau matakan hukuntad da su gaban shari’a.

A nan nahiyar Turai dai, duk `yan majalisu sun yarje kan cewar, ko kadan bai kamata a nuna wani jimiri, ga wa wannan salo na azabtad da wadanda aka tsare, ake kuma tuhuma da aikata laifuffuka ba.