1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Houthi sun hallaka wani kwamandan Saudiyya

Kamaluddeen SaniDecember 14, 2015

Mayakan kungiyar 'yan Shi'an ta Houthi da ke rike da birnin Sana'a sun ayyana cewar sune suka hallaka wani babban kwamandan kasar Saudiyya da ke aiki da dakarun gwamnatin kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/1HN4w
Jemen Huthi Rebell in Sanaa
Hoto: Reuters/M. al-Sayaghi

Kanar Abdullah Al -Sahyan wanda ke jagorantar rundunar Saudiyya a Yemen ya mutu ne sakamkon wani makami da 'yan tawayen Houthi suka harba kan sansanin sojojin da ke a Lardin Taiz na yeman ata cewar wata majiya da ke futowa daga kasar.

Ana dai sa ran a ranar talatar nan ce 'yan tawayen Houthi da jami'an gwamnatin Yeman za su yi wani zaman tattaunawa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Switzerland domin kawo karshen yamutsin watanni tara da kasar take fama da shi.