1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Haftar na san kashi a Libiya

April 29, 2019

A kokarin kare birnin Tarabulus, sojojin gwamanti a Libiya na kai wa bangaren tawaye farmaki. Makonni uku ke nan da ake gumurzu kan ikon birnin.

https://p.dw.com/p/3HbN3
Libyen | Libyens international anerkannte Regierungstruppen schießen bei Kämpfen mit östlichen Truppen in Ain Zara
Hoto: Reuters/A. al-Sahili

Dakarun bangaren gwamnati da kasashen duniya suka amince da shi a Libiya, sun kai hare-hare kan mayakan madugun yakin kasar Khalifa Haftar a ranar Lahadi, a kokarin kare Tarabulus babban birnin kasar.

Bayanani na cewa sojojin gwamnatin na Libiya, sun bi na bangaren Khalifa Haftar ne gida-gida a wasu sassa na kudancin birnin, inda ake cewa suna samun nasara. Dakarun sun badda sawu ne, cikin kayan gida suka yi ta buda wuta kan mayakan na Haftar.

Wasu ma daga cikinsu sun yi amfani da manyan bindigogin kakkabe jirage, wadanda daga bisani suka zazzaro su daga cikin manyan motocin dakon kaya da suka shiga yankin da su.

Makonni uku da suka gabata ne dai mayakan Khalifa Haftar, suka fara tsananta kai hare-haren neman kwace ikon birnin na Tarabulus.