1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayaka a Libiya sun kama jami'an Turkiyya

December 22, 2019

Daya bangaren da ke jagorantar lamura a Libiya ya sanar da kama wani jirgin ruwa dauke da jami'an kasar Turkiyya, yayin da gwamnatin Turkiyya ta bayyana hada kai da bangaren Fayez al-Sarraj.

https://p.dw.com/p/3VEU4
Tripolis Regierungssoldaten Vorbereitung Gegenoffensive
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Dakarun da ke biyayya ga madugun yakin kasar Libya, Khalifa Haftar, sun ce sun kama wani jirgin ruwa dauke da jami'an kasar Turkiyya. Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i kalilan bayan hukumomin Turkiyya sun sanar da cimma yarjejniya da bangaren gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi.

Kakakin bangaren Khalifa Haftar, Ahmed al-Mesamri, ya wallafa bayanin kame jirgin na ruwa a gabashin birnin Derna, cikin wani sakon da ya yada a shafinsa na Facebook, sai dai bai yi wani bayani mai tsawo ba. Haka nan an ga wasu hotunan bidiyo a shafin, lokacin da ma'aikatan jirgin Turkawa, ke amsa tambayoyi.

Babu dai wani tabbaci kan halin da suke ciki, kamar yadda su ma mahukuntan Turkiyya ba su kaiga cewa komai ba.