1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arziki duniya ya samu rauni saboda Coronavirus

Abdourahamane Hassane
March 27, 2020

Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva ta ce tattalin arzikin duniya ya shiga mawuyacin hali na samun koma baya saboda annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3a9WN
 Kristalina Georgieva  Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF
Kristalina Georgieva Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMFHoto: Getty Images/M. Wilson

Shugabarta asusun na IMF ta ce abubuwa za su laace fiye da yadda ake tsamanin ganin irin yadda za a dauki lokaci mai tsawo ana jin matsin na tattalin arzikin. Shugabar ta ce kasashe masu tasowa za su bukaci tallafi na dala 2500 domin yin aikin raya kasa. Yanzu haka an fara samun sabani a nahiyar Turai a kan batun tattalin arziki tsakanin kasashen kudu da na arewaci. Yayin da Italiya da Spain da Faransa da wasu sauran kasashen Turai ke son kasashen su karbo rance kudi na bai daya saboda matsalar ta tattalin arziki da ake fuskanta. Jamus da Hollande na yin dari-dari.