1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin ICC game da ɗan Ghadafi

Spencer, KimballApril 5, 2012

Kotun duniya ta nemi gwamnatin Libya ta mika mata Saif al-Islam, ɗan marigayi Gadhafi ba tare da ɓata lokaci ba, domin ya fiskanci shari'a.

https://p.dw.com/p/14Y0D
FILE - In this Friday, Nov. 21, 2008 file photo, Seif al-Islam Gadhafi, the son of Libyan leader Moammar Gadhafi, poses during an interview in New York. Moammar Gadhafi's son Seif al-Islam, the only wanted member of the ousted ruling family to remain at large, was captured as he traveled with aides in a convoy in Libya's southern desert, Libyan officials said Saturday Nov 19, 2011. (Foto:Bebeto Matthews, File/AP/dapd)
Saif al-IslamHoto: dapd

Kotun duniya da ke hukunta manyan laifukan yaƙi ta nemi majalisar wucin gadin Lybiya ta miƙa mata ɗan tsohon shugaban ƙasa wato Saif al-islam domin fiskantar shari'a. Wannan mataki da kotun da ke hague ta ɗauka, ya biyo bayan watsi da ta yi da bukatar birnin Tripoli na jinkirta miƙa ɗan marigayi Ghaddafi. shi dai Sail al-Islama ya na daga cikin waɗanda kotun ta duniya ta ke zargi da kisan kiyashi lokacin da guguwar neman sauyi ta kaɗa a Lybiya a shekarar da ta gabata.

Ita dai majalisar wucin gadi ta so ne ta gudanar da shari'ar Saif al-islam a gaban wata kotu ta Libya. Hukuncin kisa za a yanke masa a cikin Libya idan aka same shi da laifin da ake zarginshi da aikatawa, yayin da a kotun duniya kuwa, za a yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal