Matsaya kan kafa gwamnatin hadin guywa a Jamus
November 27, 2013Sa'o'i 18 jam'iyyun CDU/CSU da kuma SPD suka shafe shuna shawarwari tsakaninsu kafin su amince su jera tare cikin shekaru hudu masu zuwa. Wannan dai ba shi ne karo farko cikin tarihin Jamus ba, da bangarorin biyu suka hada guywa domin tafiyar da harkokin mulki. Ko da a wa'adinta na farko, sai da Angela Merkel ta CDU ta jera da Jam'iyyar ta SPD. Sai dai kuma a wannan karon, gwamnati ba za ta fara aiki ba, sai idan magoya bayan jam'iyyar SPD sun kada kuri'ar raba gardama kan dacewar jerawa da Merkel tsakanin ranakun shida zuwa 12 ga wata Disemba.
Sai dai kuma Klaus Shubert, malamin kimiyar siyasa a jami'ar Münster ya ce babu tabbas game da samakon kuri'ar saboda banbance-banbance da ke tsakanin SPD da kuma CDU/CSU. ya ce " Shugaban SPD na karshen da ya samu karfin fada a ji shi ne Willy Brandt, wanda ya yi amfani da gogewarsa ta siyasa wajen cimma burinsa. Amma shi ma na yanzu wato Siegmer Gabriel, ya dauki tsawon lokaci wajen ganin cewa kwalliyarsa ta mayar da kudin sabulu,ta yadda magoya bayan jam'iyyar za su yi na'am da matakin da uwar jam'iyya ta dauka"
Manufon da sabuwar gwamnati za ta sa a gaba
Ministoci 15 sabuwar gwamnatin ta Jamus za ta kunsa: tara daga cikinsu za su fito ne daga bangaren masu ra'ayin rikau wato CDU da CSU, yayin da jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gurguzu za ta tashi da kujerun ministoci shida.
Daga cikin manufofin da gwamnatin hadin guyawar za ta sa a gaba, har da kayyade Euro 8,50 a matsayin mafi karancin al'bashi da kowani ma'aikaci ya kamata ya samu a kowani awa. Da ma dai Jam'iyyar SPD da ta zo ta biyu a zaben watan Satumba, ta nace kai da fata sai a amince da mafi karancin albashi matikar ana so ta shiga cikin gwamnatin hadin guywa. Sai dai bangaren Merkel na nunawa cewa zai iya jawo nakasu ga tattalin arzikin wannan kasa, a inda zai haifar da asarar guraben aiki.
Wani muhimmin batu da jam'iyyar SPD ta nace a yi la'akari da shi a wa'adin mulki na gaba, shi ne inganta tsarin pensho na ma'aikatan da albashinsu bai taka kara ya karya ba. Wannan ya na nufin cewa za a bai wa wadanda suka shafe shekaru 45 suna aiki damar yin ritaya a shekara 63 maimakon shekaru 67 kamar yake yanzu haka.
Yawan kudi da gwamnatin Jamus za ta kashe
Aiwatar da wadannan manufofin da jam'iyyun CDU/CSU da kuma SPD suka sa a gaba, ta na bukatar kudi kimanin miliyan dubu 23 na Euro cikin shekaru hudu masu zuwa. Sai dai kuma Gustav Horn, darektan cibiyar tattatalin arziki ta IMK da ke Düsseldorf ya ce wadannan kudade ba za cire wa Jamus kitse a wuta ba. Dalili kuwa shi ne "Muna da wata babbar matsala a Jamus, wacce ba wata ba ce illa lalacewar hanyoyi. Ana ta shigar da kararraki game da wannan batu. Amma kuma ba abin da aka yi illa ware Miliyan dubu 23 na Euro. Wannan kashi daya ne bisa hudu na bunkasar tattalin arzikin Jamus. Za a iya cewa ba za su kai labari ba."
Passport biyu ga 'yayan 'yan ci-rina a Jamus
Sassa biyu sun yi alkawarin cewa ba za su karin ko da kwabo ba a matsayin haraji. Sannan kuma za su ci-gaba da sauke gammo bashin da ke kan Tarayyar ta Jamus. Hakazalika jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gurguzu ta nace kai da fata sai da aka amincewa cewa 'yayan baki da ake haifa a Jamus sun rike passport biyu wato daya na Jamus da kuma daya na kasarsu ta asali.
Rahoto cikin sauti na kasa
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu