1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyiyin fafutika na Chadi sun shiga mawuyacin hali

Dariustone Blaise GAT
June 21, 2018

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam a kasar Chadi sun koka bisa yadda gwamnati ke ci gaba da gallaza wa masu fafutikar kare hakkin dan Adam a kasar.

https://p.dw.com/p/301NN
Tschad Straßenszene in Ndjamena
Hoto: DW/F. Quenum

Shi dai Mahamat Nour Ahmat Ibedou babban magatakardan babbar hadaddiyar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Chadi wato CTDDH na daga cikin jerin mutanen da tun farko suka kafa jam'iyyar MPS mai mulki a yanzu haka a kasar ta Chadi kafin ya yi murabus a shekara ta 1993 da kuma shiga fafutikar kare hakkin dan Adam. Sai dai jajircewar da ya yi a cikin wannan aiki musamman ficen da ya yi wajen caccakar gwamnatin Shugaba Idriss Deby ta sanya a yau gwamnatin ta soma neman shiga kafar wanda guda da shi ta hanyar yi masa barazana iri-iri.

Tschad Straßenszene in Ndjamena
Hoto: DW/F. Quenum

Yanzu haka dai da dama daga cikin kungiyoyi kare hakkin dan Adam na cikin gida a kasar ta Chadi na nuna damuwa dangane da yadda yanayin 'yancin dan Adam ke ci gaba da tabarbarewa a kasar. Delphine Djiraibe wata lauya ce kana 'yan fafutika a kasar ta Chadi ta yi karin bayani dangane da hadarin da masu fafutika suke rayuwa cikinsa a halin yanzu a kasar ta Chadi.

Tschad Demonstrationen
Hoto: DW/D. Blaise

Yanzu haka dai tuni wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar suka kawo wa Mohamat Nour goyon baya tare da kai masa ziyara a gidansa a yayin da wasu kungiyoyin da kasa irin su Hadakar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta duniya ta FIDH suka fara nuna damuwa dangane da tabarbarewar yanayin 'yancin dan Adam a kasar ta Chadi musamman dangane da halin da Mahmat Nour Ahmat Ibedou da iyalansa suka shiga. Tuni ma dai reshen kungiyar ta FIDH na Afirka ya sanar da shirin kai karar kasar ta Tchadi a gaban kwamitin kula da kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya domin taka wa gwamnatin Chadi da birki.