Matsalolin fyade na karuwa a Jihar Katsina ta Najeriya
September 2, 2015A Nijeriya, wata mummunar tabi'a wadda a yanzu take neman zama ruwan-dare a duk sassan kasar – ita ce ta yi ma yara ‘yan mata fyade. Hakan kuwa na faruwa ne duk da dokar da Nijeriyar ta kafa ta kare hakkin kananan yara wadda ta tanadi daurin rai-da-rai ga duk wani wanda ya aikata wannan laifi.
A shekara ta 2003 Nijeriya ta rattaba hannu kan dokokin Majalisar Dinkin Duniya na kare hakkin kananan yara, kuma an zartas da wannan doka a matakin tarayya – sai dai kuma majalisun dokoki na jihohi 16 ne kacal kawo yanzu suka amince da wannan doka yayin da kungiyoyi masu fafutukar kare mata da kananan yara ke fafutukar ganin sauran jihohin 20 sun aiwatar da wannan doka. Rashin aiwatar da wannan doka ya sa a yanzu jihohi da dama na kasar kukowa da matsalolin nan na fyade ga mata kananan yara.
Jihar Katsina dai tana cikin jiohohin da suka amince da dokar wadda ta shafi fyade ga kananan yara mata, amma duk da haka a ‘yan kwanakin nan matsalar fyaden ga kanana yara tana kara munana a birane da yankunan karkara.
Sakamakon sakacin da kotuna ke yi na rashin aiwatar da hukuncin da ya dace kan wadanda ke aikata irin wadannan miyagun laifuka, wata kungiya ce a yanzu ta yunkuro mai fafutukar kare hakkin mata da kananan yara domin tabbatar da bin kadin fyaden da ake yi ma kananan yaran. Malam Gidado Sulaiman Farfaru, jagoran kungiyar Gender and Social inclusion mai kare hakkin jinsuna da masu bukata ta musamman, bayan taron manema labarai da kungiyar ta kira a Katsina
ya bayyana yadda matsalar ta fadada a jihar Katsina.