An soke babban zaben Somaliya
February 4, 2021Talla
Biyo bayan wata tattaunawa da suka yi tsakanin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed na Somaliya da Jam'iyyun adawa, sun nuna tsananin rashin yiwuwar gudanar da babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin mai zuwa.
Dage zabukan dai na zuwa ne sanadiyyar jan kafa da aka samu wajen shirya zaben gami kuma da gazawar gwamnati na dakile hare-haren da mayakan kungiyar al-Qaeda ke kaiwa ba dare ba rana.
A karon farko tun a shekara ta 1991, hukumomin na Somaliyar sun yi kokarin shirya zaben game gari tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya, amma hakan ya ci tura.