Nijar: Matsalar ruwa a garin Zaouzawa
March 23, 2021Taken ranar ruwan ta bana dai wacce ta dauko tushe tun shekarar 1993 shekaru 28 da suka gabata kenan, shi ne abin da ruwa ke nufi ga mutane da irin kimarsa da kuma yadda za'a iya kare wannan mahimmiyar kyauta. To sai dai ganin samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'umma nauyi ne da ya rataya a wuyan shugabanni, a wanan karni ruwa da ake ma taken abokin aiki inji yan karin magana, a garin Zaouzawa da ke makwabtaka da inda kamfanin tace man fetir din kasar na SORAZ ya tanadi runbun tsimi na gubar man fetir, al'umma na fama da matsalar ruwa.
Yayin da wakilan tashar DW suka kai ziyara garin na Zaouzawa, sun riski cincirindon mata da kananan yara dauke da jarkoki a bakin fanfon garin kwaya daya tilo da ake da shi a garin, inda wakilin rabon ruwan ya ce a irin wanan lokaci na shigar bazara fanfon na kafewa. Hakan ya sanya al'ummar garin ke hada kai wajen hana bai wa dabbobi ruwan fanfon sai dai na rijiya. A yanzu dai talakawan sun zura na mujiya kuma sun kasa na zomo, suna jiran lokacin da za su yi bankwana da wanan matsala.