Matsalar kiwon lafiya a Afirka
August 27, 2014Asusun na UNICEF ya nunar da cewa kasashen Gini da Laberiya da Saliyo da Najeriya da kuma Jamhuriyar Dimokwaradiyyar Kwango da ke fama da annobar cutar Ebola na fama da rashin yanayin kiwon lafiya mai inganci. Mai bada shawara a kan taimakon gaggawa ta asusun Heather Papowitz ce ta bayyana hakan ahirar da ta yi da manema labarai, sai dai ta ce akwai fatan samun ci gaba.....
"Matakan da suke dauka yanzu na nuna alamun samun ci gaban da ba za a rasa ba yana kuma dan farfado da fannin kiwon lafiyar, ina ganin nan gaba koda za a samu sake bullowar cutar ta Ebola ko amai da gudawa ko kyanda ko kuma zazzabin cizon sauro Malaria, za su samu kayan aikin da ake bukata domin dakile cututtukan ba kamar yanzu ba."
A wani labarin kuma jami'in jinyar nan dan kasar Birtaniya da ya kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo na can na karbar maganin da aka samar na gwaji domin magance cutar Ebolan wato ZMapp a wani asibiti a birnin London. Kawo yanzu dai babu wani tabbaci da ake da shi cewa maganin na ZMapp zai iya magance cutar Ebolan da ta adabi kasashen yankin yammacin Afirka.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu