1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HDM: Matashiya mai sana'ar gwanjo

May 28, 2020

Wata matashiya a Jihar Katsinan Najeriya ta rungumi sana'a sayar da kayan gwajo na tufafi domin dogaro da kai bayan da ta kasa samun aiki bayan kammala karatunta a Jami'ar Jihar Katsina.

https://p.dw.com/p/3crJk
Nigeria Händler von Gebrauchter Kleidung
Hoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba


A Najeriya wata matashiya mai suna Aruthoho Mercy Oghenereke a Jihar Katsinan Najeriya ta tungumi sana'ar sayar da kayan gwajo na sawa dan dogaro da kai.ta da ta kammala karatun jami'a a Jihar Katsina babu aikin yi me suna Aruthoho Mercy Oghenereke ta kama sana'ar saida kayan kwanjo na sawa dan dogaro da kai. Matashiyar wacce ta rungumi wannan sana'a bayan kammala karatu a Jami'ar Katsina na yanzu haka yawo da kayan a buhu tana bin wuraren taron jama'a dan yin talla. Yanzu haka dai matashiyar ta ce ta samu nasarori sosai saboda tana daukewa kanta hidundumu ba sai ta dogara da wani ba. Ta kuma bayyana dalillanta na shiga wannan sana'a:

"Na shiga wannan Sana'a kawai dan dogara da kaina, na ga bai kamata in ce zan dogara da iyayena ba, ya kamata in zama me amfani a cikin al'umma maimakon in zamar masu alakakai, shi ya sa bayan na kammala karatu na ga kara in kama wannan sana'ar, duk da ba wata sana'a ba ce ta a zo a gani. Ka san bayan ka gama aMsar kudaden yi wa kasa hidima bai kamata ka ce za ka jira aikin gwamnati ba, ya kamata ka tanadarma kanka wani abu kafin aikin ya zo":

Duk da irin wahala da kuma kalubalaen da ke tattare da wannan sana'a ta sayar da kayan gwanjo,  Aruthoho Mercy Oghenereke, ta ce samu karuwa sosai a rayuwarta:

Nigeria Händler von Gebrauchter Kleidung
Hoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba


 "Hakika na samu gagarumar nasara a wannan sana'a, saboda lokacin da na fara na yi tunanin wahala kawai zan sha, amma da na daure sai ga shi da sannu na cimma gaci, musamman yadda na rika samun gagarumun ciniki daga matasa 'yan uwana ba ma kamar masu yi wa kasa hidima, kasan akwai su da san sauki, ni kuma kayana akwai sauki, kuma duk inda na shiga da sana'ar nan mutane na saye kuma ana kara karfafamun gwiwa"

Sai dai kuma kamar kwace sana'a, wannan sana'a ta kayan gwajo na da nata kalubalai in ji  Aruthoho Mercy Oghenereke:

"To kalubalen da nake fuskanta a wannan sana'a ba wani gagarumi ba ne, illa na rashin isashshen jari yanda zan daina yawo, dan in samu wuri daya inda zan zauna in rika aje kayan kuma in rika sayowa da yawa har wasu su rika sari a wurina suma su sayar"

Daga karshe dai Aruthoho Mercy Oghenereke ta yi kira ga matasa da su daina zama bayin ilimin bokon da suka yi, su tashi su rungumi sana'a kowace iri ce domin fitar wa kansa kitse daga wuta:

Uganda Altkleider-Händler auf dem Owino Markt
Hoto: picture alliance/dpa/Y. Tylle

  "Ka ganni 'yan watanni kadan da suka wuce na kammala yi wa kasa hidima, ba na jiran aikin gwamnati wajen gudanar da harkokin rayuwata, saboda tini na nemar wa kaina mafita dan haka idan aiki ya samu dai dai ke nan, idan kuma bai samu ba dama ban dada kaina da kasa ba cewa dole sai na samu aikin ina da mafada. shi ya sa matasa kara ku nemi mafita bawai, ban ce kar a nemi aikin gwamnati ba, amma dai yana da kyau a ce kana da sana'a waddata za ta taimaka maka da tattalin arzikin Najeriya"