1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya da ke sana’ar dinkin hannu a Maiduguri

April 22, 2020

Fatima Abubakar Sadiq matashiya ce a Maiduguri da ke sana’ar dinkin hannu da su ka hada da kwado da linzami da sauran ado da ake yiwa manyan riguna.

https://p.dw.com/p/3bGod
Nigeria Schneiderin Fatima Abubakar Sadiq

Ita dai wannan matashiya Fatima Abubakar Sadiq wacce aka fi sani da Fatima Kori mai aikin hannun ta kasance mai kokarin neman na kanta domin dogaro da kai, abin da ya sa ta koyi sana'ar aikin hannu na yiwa kayan maza ado wato kamar su kwado da linzami da kuma sauran zubin da ake yiwa manya da kananan kaya.

Wannan ya sa Fatima Kori, wadda ta kammala karatun Boko, ta shahara tsakanin takwarorinta saboda jajircewa da kuma kokarin cika alkawari a sana'ar ta ta.

An fi sanin maza da wannan sana'a amma sai ga shi mace matashiya mai ilimin zamani ta rungumi sana'ar, abin da ya sa ta baiwa mutane da dama sha'awa har wasu ma suke koya daga wajenta.

Wannan matashiya na yin aiki ba dare ba rana domin cika alkawari abin da ya sa mutane suke ribibin kai mata aiki.

Nigeria Schneiderin Fatima Abubakar Sadiq

Wasu daga cikin wadanda take yiwa aiki sun shaida cewa ta iya aiki ta yadda in ba ita ta yi musu aiki ba, ba sa jin dadi don ko irin aikin ta ake yayi yanzu haka a Maiduguri, fadar gwamnatin Jihar Borno.

Fatima Kori ta ce ta samu nasarori da dama a cikin wannan sana'a da take yi bayan kashe wutar gabanta ta koya wa wasu da dama wannan sana'a.

Sai dai tana gamuwa da matsalolin da ta zayyana min kamar haka.

Wasu daga cikin wadanda suka koyi sana'a a wajen Fatima Kori sun ce sun sami amfani sanadiyyar koyon sana'ar.

Yayinda wasu matasa ke kashe zuciya domin jiran aikin gwamnati bayan kammala karatu Fatima Kori ta ce ita kam in aikin gwamnati ne a kai kasuwa sana'ar da take ta ishe ta.