1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Yaki da ciwon hanta

January 23, 2018

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kara himma wajen yaki da ciwon hanta wajen kara yayar da kan mutane.

https://p.dw.com/p/2rMOL
DW fit&gesund - Guwi Hepatitis
Hoto: SWR

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin yaki da yaduwar cutar shawara wato Hépatites, wadda take haddasa salwantar rayukan jama'a. Ministan kula da lafiya na kasar ne Dr. Illias Mainassara ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne ta hanyar awuna jinin mutane don tantance sanin yawan mutanen dake dauke cutar domin tanada musu magani kyauta. Bisa ga neman taimakon hukumar kula da lafiya ta duniya wato OMS da dukkungiyoyin duniya masu hannu da shunni.

Gwamnati ta kuma nunar da muhimmancin sanin alamomi na cutar ta hanta, tare da tabbatar da ganin cewa kasar ta tashi tsaye wajen yaki da wannan cuta. Lokacin wani gangami an kuma haros da mutane irin nau'o'in cutar gami da hanyoyin da ake iya kamuwa da ita, da kuma hanyar iya shawo kan matsalar.