Matakin ICC kan shari'ar shugaban Kenya
October 18, 2013Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC ta kasa da kasa da ke birnin Hague na kasar Holland ta amince cewar ba lallai ne shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da ya hallarci zaman kotun ba a shari'ar da za ta fara yi masa cikin watan gobe, dangane da zargin da ta ke masa na aikata laifukan yaki biyo bayan rikicin zaben da aka yi a kasar cikin shekara ta 2007.
Kotun dai ta bayyana hakan ne a wannan Juma'ar bayan da alkalanta suka yi wani zama na musamman kan batu kuma suka bada amincewarsu.
Alkalan dai sun ce sun dau wannan mataki ne domin baiwa shugaba Kenyatta damar gudanar da aikinsa na shugaban kasa wanda ke cike da hidimomi.
Wannan mataki na kotun ta ICC dai na zuwa ne mako guda bayan da kungiyar kasashen Afrika ta AU ta ta yi wani taro inda ta amince cewar shugabannin da ke kan mulki ba za su hallarci zaman kotun ba.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal