1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: Burkina Faso ta bi sahun Mali

Schwikowski Martina ZMA/LMJ
January 28, 2022

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta dakatar da Burkina Faso sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a wannan makon. Kasa ta uku da ta fuskanci hukuncin kungiyar.

https://p.dw.com/p/46FKJ
Burkina Faso
ECWAS ko CEDEAO, ta mayar da Burkina Faso saniyar ware bayan juyin mulkiHoto: Ahmed Ouoba/AFP/Getty Images

Wannan dai shi ne karo na hudu cikin tsukin watanni 17 da aka yi juyin mulki a yankin yammacin Afirka, wato tun tun daga watan Augustan 2020. Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO kan yi martani da sanya takunkumi, duk da cewar kwararru na ganin ba za a iya cire kungiyar daga zargin zama bangaren matsalar ba. An dai fara juyin mulkin a Mali sau biyu a jere, sai Guinea kana yanzu kuma Burkina Faso. Yanzu dai lamarin ya yi tsanani, inda Majalisar Dinkin Duniya ke kira da a koma kan dokokin kundin tsarin mulkin kasar ba tare a bata lokaci ba a kuma saki Shugaba Kabore.

Karin Bayani: Ana Allah wadai da juyin mulkin Burkina

A halin da ake ciki dai hambararren shugaban na karkashin daurin talala, a cewar 'yan jam'iyarsa kuma yana cikin koshin lafiya. Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO dai, ta yi tir da halin da ake ciki a wannan kasar, wanda ya jagoranci kakaba mata takunkumi a wani taron da wakilan kungiyar suka yi. ECOWAS ko CEDEAO na daukar matakan ladabtarwa ga duk wata kasa da ke zaman mamba da ta juyawa tsarin mulkin dimukuradiyya baya, kamar yadda ya kasance a Mali da Guinea bayan da sojoji suka kwace madafun iko.

Conakry, Guinea | Mamady Doumbouya
Jagoran sojojin da suka yi juyin a mulki kasar Mamady DoumbouyaHoto: Xinhua News Agency/picture alliance

To sai ba kowa ne yake kaunar yadda kungiyar ke katsalandan cikin harkokin cikin gida na kasashe da ma matakan kakaba takunkumi ba, a cewar Boucary Compore mai goyon bayan juyin mulkin: "Matakin ECOWAS ko CEDEAO na kakabawa Mali takunkumi ba ya tsorata mu. Saboda me? Saboda muna Burkina Faso, mu 'yan Burkina masu daraja. Burkina Faso da Mali duk abu daya ne. Don haka muke adawa da takunkumi. Sojoji sun karbi mulki ne domin su warware matsaloli. Kuma abun da ya dame mu kenan. ECOWAS ki tsaya inda kike".

Karin Bayani: Halin da ake ciki bayan juyin mulki a Guinea

A shekara ta 1975 ne dai, aka kafa kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO da nufin bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin. To sai a halin yanzu ba wai tattali kawai ba, tana da alhakin kula da gudanarwar sojoji da ma dakile ringingimu. Kafin matakin takunkumin dai, kungiyar ta yi shiru game da juyin mulkin na Burkina Faso. Sai dai Alex Vines na cibiyar nazarin harkokin dimukuradiyya ta Chatham House da ke London, na da nasa ra'ayi kan batun: "Abun da ke da wuya a nan shi ne, ba ECOWAS ko CEDEAO ce ke da alhakin wadannan juyin mulkin ba. Batu ne na gwamnatoci masu rauni da kuma a yawancin lokuta sojojin da ke da karfi, inda al'umma musamman mazauna manyan birane ke goyon bayan juyin mulkin saboda wahalar da suke ciki ta karuwar rashin tsaro. Batu na gaskiya shi ne, juyin mulki da sojoji suke yi ba ya kawo zaman lafiya."

Burkina Faso | Sabon jagoran juyin mulkin soja
Al'umma Burkina Faso na nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulkiHoto: Sophie Garcia/AP Photo/picture alliance

To sai dai wasu kwararru na ganin cewar ECOWAS ko CEDEAO ba ta da wani sahihin matsayi guda, idan aka zo batun sauyin mulki da ya sabawa kundin tsarin mulkin dimukuradiyya. Ba wai juyin mulkin sojoji kadai ba har ma idan aka zo batun tsawaita wa'adin mulki na shugabanni masu tsarin mulkin sai madi ka ture, matsayin da ya zubar da darajar ECOWAS ko CEDEAO din a idanun al'ummar yankin yammacin Afirka. Shi dai hambararren shugaban kasar na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya ajiye mulki ne, bayan matsin lamba da boren kwanaki biyu na sojoji.