1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu kare Kenyatta sun bukaci a wanke shi daga kowani zargi

Pinado Abdu WabaOctober 8, 2014

Har yanzu dai masu shigar da kara a shari'ar Uhuru Kenyatta na neman hujjoji da shaidu sai dai suna gamuwa da kalubale.

https://p.dw.com/p/1DSGi
Uhuru Kenyatta Kenia Präsident
Hoto: Reuters/Peter Dejong

Lauyoyin shugaban kasar Kenya sun yi kira ga alkalan Kotun Hukunta Manyan Laifukan Yaki da ke The Hague, da su wanke duk wani zargin da ake wa shugaban bayan da ya bayyana a gabanta a wannan larabar.

Lauyan da ke kare Mr Uhuru, Mr Stephen Kaye ya yi wannan kiran ne bisa la'akari da cewa babu isassun hujjoji. A nasa waje, lauyan da ke shigar da kara Benjamin Gumpert ya jaddada cewa akwai hujjojin da da ya kamata da an bayar domin a yi shari'a amma har yanzu ba a same su ba, mai shigar da karar yana magana ne a kan takardun bankin Mr Uhuru Kenyatta da ma bayanai daga huldodin da yayi da mutane a wayar salulansa.

Mutane tara ne suka fito fili suka karfafa zargin cewa da hannun shugaban a rikicin da ya biyo bayan zabe a shekara ta 2008, ya kuma soki lamirin gwamnatin Kenya inda ya ce tana janyo koma baya a yunkurin da aake yi na tabbatar da adalci a shari'ar.

Shugaban mai shekaru 52 na haihuwa shi ne shugaba mai ci na farko da ya taba gurfana a gaban kotun na ICC, ya taba kasancewa a kotun amma ba a matsayinsa na shugaban kasa ba.