'Yan bindiga sun kashe shugaban APC na Nasarawa
November 22, 2020Talla
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ASP Nansel, ya tabbatar wa wakilinmu na Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi aukuwar lamarin.
Matsalar garkuiwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya, musamman a rewacin kasar, inda ko a jihar Zamfara, 'yan sanda sun tabbatar da yin awon gaba da mutane 30 har da limamin karamar hukumar Maru yayin da suke sallar Juma'a.