1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Take hakkin dan Adam a kokarin aikin raya kasa

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 17, 2015

Wani binciken da 'yan jarida na kasa da kasa da kuma wasu kafofin yada labarai na duniya suka gudanar ya ce ayyukan raya kasa da Bankin Duniya ke yi na tilastawa mutane yin kaura.

https://p.dw.com/p/1FAES
Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim
Shugaban Bankin Duniya Jim Yong KimHoto: Getty Images/A. Wong

Bincike dai ya nunar da cewa sama da mutane miliyan uku ne ayyukan raya kasa da Bankin Duniya ya yi a shekaru 10 da suka gabata suka tilastawa barin gidajensu, wanda masu fafutuka ke cewa ya zamo wajibi bankin ya sake tsarinsa a bangaren kare hakkin dan Adam. Wannan matsalar dai ta fi faruwa a kasashe masu tasowa musamman a Afirka. Binciken ya nunar da cewa a jihar Lagos da ke Tarayyar Najeriya gwamnati ta tilastawa al'ummar da ke zaune a Badia East, tashi daga gidajensu ba tare da sanar da su gabanin hakan ko kuma biyansu diyya ba. Haka ma a kasar Kenya dubban mutane ne suka yi korafin kan tilasta musu barin gidajensu sakamakon wani aikin raya kasa da Bankin Duniyar ya dauki nauyin gudanarwa. Al'ummomin kasashe masu tasowa da dama dai sun sanar da wadannan 'yan jarida na kasa da kasa da suka gudanar da binciken makamantan wadannan matsaloli.

Daya daga cikin ayyukan raya kasa da Bankin Duniya ke yi.
Daya daga cikin ayyukan raya kasa da Bankin Duniya ke yi.Hoto: CC/World Bank Photo Collection

Ana take hakkin dan Adam

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya sun dade suna sukan lamirin Bankin Duniyar kan rashin lura da halin da al'ummomi ke shiga sanadiyyar ayyukan raya kasar da ya ke gudanarwa. Ko da ya ke tuni Bankin Duniyar ya amince da kura-kuran bayan gudanar da nazarin ayyukan da ya yi na raya kasar, inda har shugaban bankin Jim Yong Kim ya shaidawa manema labarai a birnin Washington na Amirka cewa akwai bukatar su inganta tsarinsu na sake tsugunar da al'umma. A wata hira da ta yi da tashar DW babbar mai bincike a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch Jessica Evans, ta ce hakan kadai ba zai wadatar ba.

Tace:" Bayan da suka yi nazarin ayyukan da suka gudanar, basu koma sun tan-tance mutanen da yadda aka cutar da su ba balle a biyasu diyya yadda ya kamata."

Bukatar gyara kura-kuren baya

Ta kara da cewa dole ne su gyara kura-kurensu na baya, inda ta ce babban abin damuwar shine Bankin Duniyar na mayar da hankali ne kawai kan yadda zai fitar da kudi amma ba yadda zai yi ayyukan raya kasar ba tare da cutar da wani ba. Dangane da abunda ya faru a Lagos, mai bayar da shawara kan kare hakkin dan Adam a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International Ashfaq Khalfan cewa ya yi...

Bankin Duniya na tallafawa bangaren noma
Bankin Duniya na tallafawa bangaren nomaHoto: Geoffrey Buta

"Ya kamata ace bankin ya san za a tashi mutane daga matsugunansu, irin hakan ya faru sakamakon wani shirin raya kasa da ya dauki nauyi, yanzu kuma bankin ya sake fitar da kudi domin yin irin wannan aikin ba tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta Lagos ba ta tashi mutane daga matsugunansu ba."

A yayin wannan taron na kwanaki biyu dai shugabannin kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo za su bayyana shirinsu na farfadowa daga annobar cutar Ebola.