Shugabannin kasashen Afirka za su yi tarukan gaggawa a Masar
April 22, 2019Rahotanni daga kasar Masar sun bayyana yadda shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi zai jagoranci wasu tarukan gaggawa da shugabannin kasashen Afirka a kan yanayin da kasashen Sudan da Libya suke ciki.
Taron da zai gudana a ranar Talata zai mayar da hankali ne kan yadda zanga-zanga a Sudan ke kara kamari bayan sojoji sun hambarar da shugaba Omar al-Bashir da kuma duba hanyoyin da za a yi amfani da su don kawo karshen rikici a Libiya, kasar da kwamanda Khalifa Haftar ke jagorantar munanan hare-hare a birnin Tripoli.
Shugaba al-Sisi wanda a halin yanzu yake zaman shugaban kungiyar tarayyar Afirka, zai karbi bakonci shugaba Idriss Deby na kasar Chadi da Paul Kagame na Ruwanda da Mohamed Abdullahi Mohamed na Somaliya da Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da kuma shugabannin kasashen Kwango da Dijbouti.
Wadannan tagwayen tarurrukan gaggawa sune irinsu na farko da shugabannin kasashen Afirkan za su gudanar kan rikicin kasashen na Sudan da Libya. Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya na daga cikin wadanda za su yi jawabi a taron game da hanyoyin da za a bi don dakile ta'addanci.