Masar ta kori kocinta
September 6, 2021Talla
Ana kuma sa ran sanar da sabon kocin da zai cigaba da jan ragamar 'yan wasan na Masar nan na kwanaki biyu. Wasan raunin da Masar ta yi da Gabon a ranar Lahadin da ta gabata, inda suke bukatar dai-daita minti na 90 don kubutar da maki daya, da kuma nasarar da suka samu da ci 1-0 a kan Angola a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da suka gabata, ya haifar da suka mai zafi daga magoya bayan da ba su ji dadi ba a shafukan sada zumunta.