Musayar wuta tskanin Falasdinawa da Isra'ila
November 14, 2019Wasu rokokin Isra'ila sun yi raga-raga da wasu gidaje uku tare da halaka mutane biyar cikinsu harda wani matashi da ke shirin angwancewa a wannan makon. Adadin Falasdinawan da Isra'ila ta kashe a kwanaki biyu da fara kai hare-haren kisan dauki dai-dai kan jagororin Falalsdinun dai, a yanzu ya kai 32, cikinsu har da Baha Abul Ata kwamandan kungiyar Jihad al Islami da Isra'ilan ta fara da kasheshi shi da dansa, ta hanyar harba gwamman rokoki cikin gidansa.
Suma dai mayakan Jihad al Islamin sun yi ta harba rokoki kan yankunan Isra'ilan, inda aka sanar da jiwa wata tsohuwa rauni, da kuma bude ramukan karkashin kasa a yankunan, don samar da matsera ga masu gudu. Yunkurin shiga tsakanin da Masar ta yi dai ya jawo lafawar wuta, amma kuma ba da jimawa ba suka dawo gidan jiya.
Kungiyar Jihad al Islamin ta bayar da sharuddanta na tsagaita budewa juna wuta da sojojin Isra'ila wadanda suka hada da dakatar da hare-haren da take kai wa kan yankunan Zirin Gaza da kuma dakatar jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a yankin, sannan daga karshe dole ne ta sassauta killacewar da takewa yankin na Zirin Gaza.
Kungiyar Hamas da ke iko da yankin na Zirin Gaza, wacca kuma ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ilan tun a shekarar 2014 sakmakon shiga tsakanin da Masar ta yi, ta ce duk wani hari kan mayakan sa kai na kowace kungiyar Falalsdinawa, keta yarjejeniyar da suka cimma da Isra'ila ne, don haka ba za ta nade hannunta ga irin wannan abun da ta kira mummunan cin zalin ba.