Masana'antar buga Dalar Amirka
DW ta kai ziyara masana'antar da ta kwashi fiye da shekara 150 ta na aikin buga takardar kudin Amirka da wasu mahinman takardu na kasar.
Masana'antar buga takardun kudi
An kafa masana'antar buga takardun kudin Amirka wato The Bureau of Engraving and Printing (BEP) a birnin Washington a shekarar 1862. An kawata kofar shiga ginin da wasu manyan karafa.
Agogon dala
Baki akalla miliyan guda ne a duk shekara ke kai ziyara masana'antar, inda suke kallon ayyukan da ke gudana ta wani kebabben daki da aka tanadarwa bakin sai dai duk inda ka ke a cikin ginin za ka san masana'antar da ka shiga don kuwa ko agogon cikin ginin an yi masa ado da takardar kudin na dalar Amirka.
Inji mai buga tambari
Launin koriyar kala da ke jikin dalar Amirka ya kasance mafi dadewa da kasar ke anfani da shi a duk wasu muhimman takardun baya ga dalar. Sinadaran da aka yi anfani da su wajen hada wannan kala ya kasance babban sirri amma Ed Mejia, daya daga cikin wadanda ke da masaniya ya kasance wanda ya ke kula da zanen kudin injin na iya buga takardar kudi na dala dubu goma a sa'a guda.
Sashen shanya takardun kudi
Masana na saka ido don tabbatar da komai ya tafi daidai, takardun kudin na bukatar kwanaki uku kafin su bushe daga nan sai a aika su rumbun ajiya. Baki daya ana iya buga dala miliyan dari biyar da sittin a kowacce rana, dala uku da centi shida shi ne farashin buga dala daya.
Sashen tsaro
A wannan sashen akwai alama da ke tunatar da ma'aikata cewa aikin na gayya ne don babu wanda zai yi aiki shi kadai. Ma'aikaci na daukar albashin dala dubu casa'in da auku a duk shekara, albashin ya ninka na ma'aikacin gwamnatin Amirka.
Sashen buga lambobin kudin
Mataki na karshe kafin a fitar da takardar kudin ya kunshi buga numbar kan kowacce takarda kudi. Kowacce na dauke da lamba daban kuma ana wannan aikin ne da hannu maimakon anfani da inji.
Sashen kidaya
Nan injin ne zai kidaya kudin ya na tantance rukuninsa. Daga nan za a ware su a daure su dami-dami. Wani ma'aikaci zai kwashi kudin a wani keke inda zai baiyana bangaren da aka rubutu nambar kudin har ya zuwa lokacin da za a mika kudin ga babban bankin kasa. Ba za a iya anfani da kudin ba har sai an tantance sahihancin wadannan lambobin.
Tsaro na kan gaba
Tsaro na ma'aikatan masana'antar dubu biyu na da matukar mahinmanci a yayin da ake aikin buga kudin. Ana kammala aiki buga kudin sai a latsa wannan tambarin mai ja na alamar kammala aiki.
Barkwanci
An sanya wani rubutu na barkwanci don farantawa ma'aikata rai, rubutun na tunatar da ma'aikata kan aikin buga takardar kudi a gargajiyance don nishadantar da su. Mawallafa: Anja Steinbuch da Michael Marek.