Martanin kasashen duniya kan zaben Jamus
September 25, 2017A tsokacinsa dangane da sakamakon zaben na Jamus shugaban faransa Emmanuel Macron ya yi maraba da nasarar da Angela Merkel ta samu ya na mai taya murnar samun wa'adin mulki na biyu. Macron ya yi alkawarin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta cigaba. A nasa bangaren shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker bukatar shugabar gwamnatin Angela Merkel ya yi ta kafa kawancen gwamnati mai karfi cikin hanzari domin taimakawa wajen tabbatar da daidaiton tarayyar Turai.
Ita kuwa shugabar jam'iyyar masu ra'ayin kyamar baki ta Faransa Marine Le Pen baiyana farin ciki ta yi da ganin jam'iyar kyamar baki ta Jamus AfD ta sami shiga majalisar dokoki a karon farko da wakilai masu yawa har ma ta ce ''na yi matukar murna ganin takwarar mu ta AfD a Jamus za ta shiga majalisar dokoki ta Bundestag. Ina kuma so na baiyana cewa sakamakon da suka samu kamar irin namu ne."
A London ko da ya ke wasu jama'ar sun rika shagube da nasarar Angela Merkel a waje guda kuma sun baiyana damuwa da shigar masu kyamar baki a majalisar dokoki. Wani mazaunin birnin na London ya shaidawa manema labarai cewar ''na yi mamaki matuka da tasowar masu kyamar baki. Ban san abin da zai faru ba a gaba amma abin da ban tsoro. Ina ganin kamar tarihi ne ya ke neman maimaita kansa."