1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan taron SPD

October 29, 2007

Yan Siyasa na cigaba da furuci

https://p.dw.com/p/C14p
Kurt Beck ,Shugaban SPD
Kurt Beck ,Shugaban SPDHoto: AP

Bayan kammala babban taron kasa na yini uku na jammiiyyar SPD,inda ta gabatar da sabbin manufofinta na democradiyya ta gurguzu,wakilan jamiiyyar dama sauran yan siyasa dake nan tarayyar jamus na cigaba da tofa albarkacinsu.

Shugabar gwamnati jamus Angela Jamus wadda jamiyyar ta yan mazan jiya ke mulkin hadaka da kamiyyar ta SPD ta bayyana cewar,ba a muradin sake komowa tsarin democradiyya na gurguzu ,kamar yadda aka fuskata a gabashin turai,inda nan ne ta taso.

"Nayi dogon nazari dangane da wannan tsari,na democradiyyan gurguzu,kuma a gani na wadannan batutuwa ne biyu da bazasu taba haduwa ba,kuma zan cigaba da zama kann wannan matsayi nawa"

Babban sakataren zartarwa na jamiyya mai kawance da CSU ta merkel,watau CDU Ronald Pofall,tuni ya dasa ayar tambaya adamgane da wadannan sabbin manufofi na jamiiyar ta SPD.

"Yace wannan tsarin yayi kama da tushe irin na gurguzu na tsarin baya,domin democrtadiyya na gurguzu wani sabon tsari ne da ake darajawa.A nan jamus mun kasance a karkashin wannan tsarin na lokaci mai tsawo kuma hakan ya ishemu,kamata yay SPD ta nisantar da kanta daga wannan tsari"

Wadannan martani daga wadannan jamiiyyu da suke gudanar da mulki tare dai bai gamsar da shugaban jamiiyyar ta SPD Kurt Beck ba a karshen taron na Hamburgh.Domin acewarsa akidojin jamiyyar SPD zasu cigaba da kasancewa yanci,da adalci kazalika da hadin kai.

"Saboda wani yace bai amince da manufofi ko kuma tsarimmu ba,bazai shafemu,tun da dai dukannin wannan tsari bai danganci yanci ko kuma adalci,kamar yadda yake kunshe a akidojin jamiiyyramu ba.Don haka wadannan martani na nuna adawa,wanda ko kadana bazai shafe mu ba".

Jamiyyar masu yan mazan jiya ta CSU da mai sassaucin raayi ta SPD dake zama tsohuwar abokiyar adawarta,sun kafa gwamnatin hadin kann kasa a watan Nuwamban shekarata 2005,bayan arangama mai daci da sukayi,wanda ya haifar da rashin kammala zaben kasa baki daya.Shekaru bayan kafa wannan gwamnati bisa jagorancin Merkel dai ,tana samun karuwan goyon baya da kashi 39 daga cikin dari,idan an kwatanta da Jamiiyyar da SPD dake da kashi 26 daga cikin 100 kachal.

Da gagaruman zabe a manyan jihohin jamus guda uku a shekara mai zuwa,gabannin zaben kasa na 2009 dai,bangarorin biyu na cigaba da yakin neman zabe na sukan juna,kamar yadda suke bayyanawa a tafiyar da harkokin gwamnati.

Sai dai manazarta na ganin cewar hanya daya da jamiyyar SPD zata iya yakar Merkel dashi shine,tsoffin akidojojin jamiyyar da suka hadar da kare muhalli da kare haskkin biladama cikin diplomasiyya,zuwa inganta rayuwar Iyali.To sai dai kawo yanzu zargin da SPD ke yiwa Merkel na rashin tabuka komai,bai janyo musu karin kuriu ba.

Jaridu a sharhunan su dangane da wannan taro dai,sun bayyana cwewar bisa dukkan alamu shugaban jammiiyyar na yanzu Kurt Beck,shine kadai zai iya yin takara a shekara ta 2009,zai dai irin manufofinsa bazasu ja hankalin masu kada kuriu ba.