Najeriya: Tsare jagoran kungiyar matasan arewa
June 18, 2020Nastura Ashir Sharif ne dai jagoran gamayyar kungiyoyin matasan Arewan da suka gudanar da zanga-zangar a Katsina, kuma ana yi wa matakin da hukumomin Najeriyar suka dauka a kansa a matsayin yunkuri na toshe bakin kungiyoyin da ma ba su tsoro. Matsan dai sun shirya zanga-zangar ta lumana ne, dangane da abin da suka kira da tabarbarewar yanayin tsaro a arewacin kasar da ya sanya su neman gwamnatin kasar ta dauki mataki.
Ba gudu ba ja da baya
A ta bakin Aminu Adam da ke zaman daraktan gudanarwar gamayyar kungiyoyin laifin da ake tuhumar jagoran nasu da shi, ba ya rasa nasaba da zanga- zanga da aka yi a Katsina kuma kafin gudanar da ita sai da suka nemi izini. Ya kara da cewa: "Wannan ba zai razana mu ba, kuskuren da suka yi suna ganin kamar in an kama Nastura gwargwamayar nan ta tsaya."
Tuni dai kama jigon masu zanga-zangar ya sanya mayar da martani mai zafi daga kungiyoyin kare hakin dan Adam na Najeriyar, inda Mallam Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC ya ce hakan ya sabawa hakkokinsa na dan kasa, kuma a hanzarta sakin sa. Mummunan hali da yanayin tsaron Najeriyar ya shiga a kasar musamman a yankin arewaci, ya kasance babban kalubale da ke fuskantar jama’a a yanzu. To sai dai ga Dokta Suleiman Shu'aibu Shinkafi da ke cikin kungiyoyin da ke faftuka a kasar, ba fa za a doke su a hana su kuka ba.
Tura ta kai bango
Wakilinmu a Abuja Uwais Abubakar Idris ya yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriyar, domin jin dalilan kama Nastura Sharif amma sun ki cewa uffan a kan batun, kuma har kawo yanzu jagoran matasan na hannun 'yan sandan a Abuja.
Yerima Shettima shugaban tuntubar matasa ya ce akwai alama da kokarin sakin Nastura domin ana jiran a kai shi ya gana da sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar. Ga Hauwa Mohammed Kabir da ke cikin masu gwagwarmayar, tura fa ta kai bango. Za dai a saka ido a gani ko kama jigon zanga-zangar zai sa su ja baya da matsin lambar da suke ga gwamnati a kan bukatar daukar mataki, inda tuni shugaban kasar ya bayar da umurni na sake duba batun da ya zamewa kasar abin kunya.