Martani a bayan zaben Majalisar Turai
May 26, 2014Cikin dare ne a jiya aka sanar da sakamakon zaben majalisar Turai da aka gudanar a nan Jamus da mafi yawan kasashen kungiyar hadin kan Turai. A cibiyoyin manyan jam'iyun siyasa na Jamus, wakilai sun baiyana farin cikin sakamakon da suka samu, musamman a hedikwatar jam'iyyar Social Democrats, wato SPD, inda shugaban majalisar Turai, Martin Schulz yayi wa magoya bayansa jawabi kafin ya zarce zuwa Brussels.
Kimanin awa guda da rabi bayan rufe rumfunan zabe, aka sami mafi yawan sakamakon kuri'un da aka kada, inda aka fahimci cewar jam'iyar Social Democrats, wato SPD tana daga cikin mjam'iyun da suka fi samun nasara a zaben. Dangane da haka ne da yake jawabi a cibiyar jam'iyarsa, shugaban SPD, Sigmar Gabriel yace:
"Karin goyon bayan da muka samu shin mafi girma d jam'iyar SPD ta taba samu a wani zabe na Jamus baki daya. Wannan nasara kuwa ta samu ne godiya ta tabbata ga mutum daya, wato Martin Schulz."
A nashi martanin kan wannan yabo, Schulz yace nasara dai ba a taba dora ta kan mutum guda kawai. Wannan nasara ce da ta nunar da yadda democradiya take, da kuma bukatar sabunta nahiyar Turai baki daya. Shugaban majalisar Turan yace saboda haka ne jam'iyarsa take ganin dacewar zabensa a matsayin shugaban hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai na gaba.
A daya hannun, jam'iyar Christian Democrats, wato CDU, tayi asarar wani bangare na kuri'un da ta samu, amma taci gaba da kasancewa jam'iyar siyasa mafi karfi a Jamus, ko ma bayan zaben na Turai a jiya. Yayin da jam'iyar SPD ta sami kashi 27.3 ne a zaben, ita kuwa jam'iyar CDU da kawarta CSU sun sami misalin kashi 36 ne cikin dari. Duk da haka, babban dan takarar jam'iyun, David McAllistr ya nunar da cewar:
"Babu shakka mun cimma burin da muka sanya gaba a wannanzabe. Abin da muka so shine mu ci gaba da da zama jam'iya mafi karfi a zaben, mu kasance a gaban SPD. Mun kuwa sami nasarar haka. Mu ne na daya, mu ne muka sami nasarar wannan zabe, abin dake tabbatar da goyon baya ga manufofin jam'iyun CDU da SCU a nan Jamus da nahiyar Turai.
Wata jam'iyar da ta sami kyakkyawar nasara a zaben na majalisar Turai a Jamus, ita ce jam'iyar yan kishin kasa dake kyamar manufofin nahiyar Turai, wato AfD ko kuma Alternative für Deutschland. Jam'iyar da a karon farko kenan ta shiga zaben Turai, kai tsaye ta sami kashi bakwai cikin dari na kuri'un da aka kada, yayin da jam'iyar Greens ta masu da'awar kare muhalli ta sami kashi 10.7 cikin dari, sa'annan jam'iyar FDP ta tashi da kashi uku da digo hudu cikin dari na kuri'un da aka kada.
Gaba daya dai a nahiyar Turai, jam'iyu na yan kishin kasa masu kyamar manufofin nahiyar Turai da kyamar baki sun sami karin goyon baya, musamman a Faransa, inda jam'iyar Front Nationale ta Marie Le Pen tafi samun goyon baya ko kuma a Ingila, inda jam'iyar UKIP ta sami kuri'u masu yawa. Bayan zaben na jiya, jam'iyu masu ra'ayin yan mazan jiya suka fi samun kujeru a majalisar, inda gaba daya za su sami misalin kujeru 212, yayin da jam'iyar Social Democrats da yan gurguzu suke da kujeru197, yayin da jam'iyun hadin gwiwa masu kyamar Turai zasu tashi da misalin kujeru 140 a sabuwar majalisar ta Turai.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal