Manyan 'yan wasa da suka kamu da HIV
Cutar HID/AIDS na shafar 'yan wasa, kuma ta yi sanadin rasuwar wasunsu. Wasu kuma kamar Earvin Johnson da Greg Louganis da suka fito daga Amurka sun shafe kimanin shekaru 30 dauke da cutar.
Tom Waddell - Wanda ya kirkiri wasannin masu neman jinsi guda
Waddell ya yi wasa a gasar Olympics ta shekara 1968 da aka yi a kasar Mexico, inda ya zo na 6. Dan wasan ya karanci aikin likita, inda ya kammala a shekarar 1982. Waddell wanda mai neman jinsi daya ne ya shirya wasanni na masu neman jinsi guda a San Francisco don kawar da kyamar da ake yi musu. A 1985 ce aka gano yana dauke da cutar AIDS, inda ya rasu a shekarar 1987.
Michael Westphal - Ya rasu sanadiyyar cutar da ba a san irinta ba
A shekarun 1980 Westphal ya yi fice a wasan Tennis a kasar Jamus. Shi da Boris Becker sun taka rawar gani a lokacin don har wasan karshe suka kai a gasar Davis Cup a shekarar 1985 ko da dai ba su yi nasara ba. Daga baya Westphal ya kamu da rashin lafiya kuma ba a gane asalin cutar ba. A shekarar 1991 cutar AIDS ta yi ajalinsa amma sai bayan shekaru goma da rasuwarsa budurwarsa ta bayyana hakan.
Earvin “Magic” Johnson - Fitaccen mai yaki da HIV da AIDS
Duniyar wasanni ta kadu a lokacin da dan wasan kwallon kwandon ya sanar da cewar yana dauke da HIV a shekarar 1991. Johnson (na biyu daga dama) ya dakatar da yin wasa amma ya ci gaba a shekarar 1992 har ma ya lashe labar yabo ta Zinare a wasannin Olympics da aka yi a Barcelona. Duk da cewar ya kai shekaru 65, Johnson na ci gaba da gwagwarmaya wajen taimakon masu cutar.
Arthur Ashe ya kamu da HIV da aka yi masa karin jini
A shekarar 1975 ce Ashe ya zama bakar fata na farko da ya lashe gasar Wembledon mai darajar gaske. Kafin wannan nasara da ya samu, ya lashe gasar Australian Open da US Open. A shekarar 1983 aka yi masa karin jinin da ke dauke da kwayar cutar HIV, bayan da aka yi masa aiki a zuciyarsa. A shekarar 1992 ce ya bayyana cewa yana dauke da cutar, kana ya rasu a shekarar 1993.
John Curry - Mutumin da Jaridar Bild ta ce mai neman jinsi daya ne
Curry fitaccen dan wasan takalmin taya ne da ya zama gwarzo a Turai da ma duniya baki daya a shekarar 1976, har ya kai ga lashe lambar yabon ta Zinare a gasar Olympics din shekarar wa da aka yi a Innsbruck. Kafin wannan nasarar da ya samu, Jaridar Bild ta bayyana cewar mai neman jinsi guda ne. A karshen shekarar 1987 aka bayyana cewar ya kamu da kwayar cutar HIV kuma ya rasu a shekarar 1994.
Greg Louganis - Mutumin da ya samu nasarori duk da cewa yana da HIV
Louganis ya samu damar lashe labar yabo ta zinare a wasan ninkaya a gasar Olympics ta shekarar 1984 da aka yi Los Angeles da wanda aka yi 1988 a Seoul. A shekarar 1994 ce ya bayyana cewar shi mai neman jinsi guda ne kuma yana dauke da kwayar cutar HIV. Zuwa yau da yake da shekaru 64 da haihuwa, Louganis na ci gaba da fafutuka wajen inganta rayuwar masu dauke da cutar AIDS.
Rudy Galindo - Ya kula da dan uwansa mai cutar AIDS
An haifi Galindo a shekarar 1969. Ya kula da dan uwansa mai dauke da AIDS har ya rasu a shekarar 1994. Masu horas da shi guda biyu ma sun rasu sanadiyyar cutar. Shi kansa ya kamu da AIDS din a shekarar 2000 bayan da ya bayyana cewar shi mai neman jinsi guda ne.
Gareth Thomas - Ya dau shekaru kafin ya bayyana cewar yana da HIV
Thomas ya yi wa yankin Wales wasan zari-ruga akalla sau 100 a lokacin da yake sharafinsa. A karshen shekarar 2009 ce ya zama dan wasan zari-ruga na farko da ya fito ya ce shi mai neman jinsi guda ne. A shekarar 2019 ce kuma ya bayyana cewar yana dauka da kwayar cutar HIV, inda ya ce shafe shekaru yana dauke da ita.