Manya masu guje wa haraji
November 6, 2017Talla
Wasu bayanan sirri kan harkokin kudade sun kwarmato yadda wasu manyan mashahuran mutane ke zuba jari a wasu wuraren da ake ganin suna gujewa biyan haraji ne. Bayanan da ake wa lakabin 'Paradise Papers', sun ce sakataren harkokin kasuwancin Amirka Wilbur Ross na da wata harkar da ya ke yi da wani kamfanin jiragen ruwa da ke da alaka da shugaba Putin na Rasha.
Bayanan haka nan sun bayyana yadda wasu kamfanonin sarauniyar Ingila suka zuba jari a wasu wuraren da babu biyan haraji. Paradise Papers din dai na da bayanai sama da miliyan 13, kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta nan Jamus ta bayyana.