1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangamar 'yan sanda da manoma a Indiya

Abdul-raheem Hassan
February 13, 2024

'Yan sanda sun yi arangama da manoma masu zanga-zanga a kan iyakar birnin New Delhi a kasar Indiya, jami'an tsaron sun tarwatsa masu zanga-zangar a yayin da suke yunkurin kutsa kai cikin babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4cLvp
'Yan sandan Indiya
Hoto: Manish Swarup/AP Photo/picture alliance

Manoma wadan da galibi daga jihohin Haryana da Uttar Pradesh da Punjab, sun fara tattaki zuwa fadar gwamnatin kasar a ranar Talata don tabbatar da tallafin kudaden ayyukan noma. Ɗaya daga cikin mahimman buƙatun manoman kasar shi ne matsawa gwamnati lamba ta samar da dokar rage farashin kayan amfanin gona.

Akalla manoma 600 sun mutu a shekarar 2020, yayin wata zanga-zanga da zaman dirshen da manoman suka yi na tsawon shekara daya a kan iyakar babban binrin kasar inda suke nuna adawa da dokar farashin bai daya na amfanin gona a kasar.