Manoma a Indiya sun bukaci karin farashi
March 14, 2024Talla
Zanga zangar manoman na zuwa ne wata guda bayan da suka yi sansani a arewacin kasar inda yan sanda suka dakatar da su daga shiga birnin na Delhi.
Karin Bayani: Zanga-zangar manoma na kara zafafa a Indiya
Wannan na faruwa ne yayin da ake sa ran nan da yan kwanaki gwamnatin ta Indiya za ta yi kiran sabon zabe da ake sa ran Firaministan kasar Narendra Modi zai sake neman tazarce a karagar mulki a karo na uku.