Mandela ya mamaye kanun labarai a Jamus
December 13, 2013A sharhinta game da gagarumin bikin da aka yi na ranar Talata na juyayin mutuwar tsohon shugaban Afirka Ta Kudu, Nelson Mandela, jaridar Süddeutsche Zeitung tace wannan biki a Johannesburg ya zama taron koli ne na musamman, saboda kamar yadda tace, taron na juyayi game da mutuwar gwazon na Afika ta kudu, ya hade shugabannin kasashe wuri guda wadanda bisa al'ada manyan abokan gaban juna ne. Ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska, basu hana shugabanni daga akalla kasashe 90 su halarci bikin na juyayin mutuwar Mandela a babban filin wasa na Johannesburg ba, gaban msu zaman makoki kimanin dubu 90 da miliyoyi a ko ina cikin duniya. Nelson Mandela, wanda yayi zaman kaso na tsawon shekaru 27, kafin a sake shi a shekarata 1990, a kuma zabe shi kan mukamin shugaban kasa a shekara ta 1994, ya rasu ne ranar Alhamis ta makon jiya bayan rayuwar shekaru 95 a duniya. Ranar Lahadin nan za'a yi jana'izarsa.
Jaridu da dama sun yi sharhuna a wannan mako kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Jaridar Neue Zürcher Zeitung misali, tace kokarin da sojoin Faransa suke yi na karbe makamai daga hannun yan tawayen kasar, ya zama abu mai wahala da ya jefa ta cikin mummunan hali na yakin basasa. A makon jiya, birnin Bangui ya zama dandalin kisan kare-dangi, musamman kan musulmi. Jaridar tayi magana game da dubban yan gudun hijira da yakin ya rutsa dasu, wasu kuma aka kore su daga wuraren zamansu na asali, kuma suke rayuwa yanzu a wani mummunan hali kusa da tashar jiragen saman Bangui.
A daya hannun, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace Faransa ba da zuciya daya ta tura sojojin ta su kwace makamai daga hannun yan tawayen Seleka a kasar ta Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya ba. Kasar ta Faransa tsawon fiye da shekaru hamsin kenan take amfani da sojoji domin kare bukatunta a kasashen Afirka da ta taba yi masu mulkin mallaka. Kasar ta dade tana bada kariya ga shugabannin Afirka yan mulkin kama karya, muddin zasu cimma bukatnta na tattalin arziki.
A nata sharhin, jaridar Tagesspiegel tace sannu a hankali ana gani kasar Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya tana rushewa. Bayan kasar tayi shekara da shekaru tana fama da tashin hankali, yanzu kuma sai gashi sojojin ketare ne wai zasu kawo zaman lafiya a cikinta. Jaridar Tageszeitung tayi tambayar shin abin da bai yiwu jiya ba, ta yaya za'a same shi a yau.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba batun cin rashawa ne, inda tace kamfanin gine-gine na Jamus wato Bilfinger an tilasta masa biyan tara ta kudi dollar miliyan 32 a Amirka, saboda laifin bada toshiyar baki a Najeriya. Binciken hukumar FBI a Amrika ya gano cewar kamfanin na Bilfinger tare da hadin gwiwar wani kamfani na Texas mai suna Wilbros da ya kware wajen shimfida bututun mai, sun bada cin hanci ga jami'an gwamnati a Najeria, kafin kamfanonin biyu su sami kwantaragin na adadin kudi dollar miliyan 387 tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2005, sai da suka baiwa jami'an gwamnatin Najeriya hanci na kudi dolar miliyan shida. Kamfanin Bilfinger an san shi da sunan Julius Berger ne a Najeriya, kuma shine kamfani mai zaman kansa da yafi daukar ma'aikata a kasar.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar