1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malta ta kwato jirgin ruwan da aka kama

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2019

Jami'an tsaron kasar Malta sun yi nasarar kwato jirgin ruwan dakwon man fetur din nan wanda 'yan gudun hijira suka kwace a saman teku daga hannun matukansa bayan da jirgin ya ceto su a saman tekun.

https://p.dw.com/p/3Fp6c
Malta Valetta Flüchtlinge auf gekapertem Handelsschiff Elhiblu I
Hoto: Reuters/D.Z. Lupi

Yanzu haka dai tuni a wannan Alhamis jami'an tsaron kasar ta Malta wadanda suka yi nasarar kwato jirgin ruwan daga hannun 'yan gudun hijirar a daren jiya suka iso da shi a tashar ruwan Valette ta kasar ta Malta. 

A ranar Talatar da ta gabata ce dai jirgin ruwan dakwon man fetur din mai suna Elhiblu ya ceto 'yan gudun hijira 108 da suka hada da mata da kananan yara 31 a saman teku. Amma kuma 'yan gudun hijirar masu burin shiga Turai suka kawace iko da jirgin a lokacin da yake kokarin mayar da su a kasar Libiya tare da juya akalarsa zuwa gabar ruwan Italiya. 

Tuni dai kuma aka mika wadannan 'yan gudun hijira a hannun 'yan sandan kasar ta Malta domin gudanar da bincike neman sanin takamaiman abin da ya wakana da kuma wadanda ke da alhakin a cikin matakin kwace jirgin.