1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malala ta wallafa hotunan aurenta

Ramatu Garba Baba
November 10, 2021

Labarin auren Malala Yousufzai 'yar fafutikar ilmin yara mata da ta tsallake rijiya da baya bayan harin 'yan Taliban da ke adawa da ilimin Boko ya karade shafukan sada zumunta.

https://p.dw.com/p/42o5s
Malala Yousafzai | Tokyo, Japan
Hoto: Rodrigo Reyes Marin/ZUMA/imago images

Malala Yousufzai matashiyar 'yar fafutikar ganin yara mata sun je makaranta a Pakistan ta sanar wa duniya labarin auren ta da Angonta mai suna Asser Malik, an wayi garin wannan Laraba da sakon da ta wallafa a shafinta na twitter inda miliyoyin mabiyanta suka yi ta taya ta murna.

Malala ta fito idon duniya a shekarar 2012  bayan da ta tsallake rijiya da baya, a lokacin da wasu 'yan Kungiyar Taliban suka yi yunkurin kashe ta, bayan da suka harbeta da bindiga a ka, an yi nasarar ficewa da ita daga kasar Pakistan zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya inda aka yi ma ta magani, sai dai ta ci gaba da zama a can a sakamakon barazanar da ta ke fuskanta daga Taliban da sauran kungiyoyi da ke adawa da ilimin Boko.

Yar asalin kasar Pakistan mai shekaru 24 da haihuwa, ta kasance yarinya mafi karancin shekaru da ta karbi lambar yabo ta Nobel. Ta shahara a duniya inda ta ke ci gaba da gwagwarmayar ganin an bai wa kowacce 'ya mace damar samun ilimi.