1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar siyasar Hama bayan hukuncin kotu

Mahaman Kanta
March 14, 2017

Hukuncin shekara guda da kotu ta yanke wa Hama Amadou kan badakalar cinikin jarirai ya sa magoya bayansa na ganin cewa wani bita da kulli ne domin mayar da shi saniyar ware a fagen siyasar Nijar.

https://p.dw.com/p/2Z90S

Hama Amadou ya yi zaman watanni biyu a gidan kaso kafin rashin lafiya ya kamashi, wanda ya sa aka bashi damar tafiysa Faransa. Sama da mutanen 30 ne badakalar jariran ta shafa, kuma aka yanke musu hukunci ciki har da Hama Amadou. Sai dai Lawyoyinshi suka ce ba yi shari'ar bisa ka'ida ba. Tuni dai wannan hukuncin ya haifar da muhuwara a Jamhuriyar Nijar

Magoya bayan Hama Amadou suka ce bita da kulli ake yi wa gwarzonsu don a kawar da shi a fagen siyasa, kamar yadda Hassane Saleh Amadou, jigo a jam'iyyar Lumana ya ce. "Saboda a hanashi yin siyasa ne aka yanke masa wannan hukunci."
Sai dai Ibrahim Massaoudou, wani mai fashin baki a fagen siyasar Nijar ya nunar da cewar "akwai gagangu 'yan siyasa da suka fuskanci tuhume-tuhume na kotu tare da shan dauri, amma kuma suka samu ikon yin mulkin kasashensu."

Mutum daya ne aka kai gidan kaso kai tsaye daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci a badakalar cikin jarirai ta NIjar.