Makarantu a Gini sun buda kofofinsu
February 13, 2015A kalla makarantu dubu 12 na kasar suka buda kofofinsu daga ranar 19 ga watan Janeru da ya gabata kawo yanzu a cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF. An dai rufe makarantu sakamakon yaduwar cutar ta Ebola a kasashen Liberiya, Saliyo da kasar ta Gini da suka fi fama da wannan cuta. A ranar Litinin mai zuwa ce ake sa ran komawa ga makarantun na boko a kasar Liberiya, yayin da a watan Maris mai zuwa ake sa ran komawa ga makarantun a kasar Saliyo. Sai dai kuma labarun baya-bayannan na cewa an killace gidaje a kalla 700 har na tsawon kwani 21 a garin Aberdeen da ke kasar ta Saliyo, bayan rasuwar wani mai kamun kifi da aka gano cewa cutar ta Ebola ce ta kashe shi.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleyman Babayo