1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makami kirar Rasha ya harbo jirgin Malesiya a Ukraine

Gazali Abdou TasawaOctober 13, 2015

Sakamakon bincike da wata cibiyar kasar Holland ta yi kan faduwar jirgin Malesiya Airlines a Ukraine a shekara ta 2014 ya nunar da cewa an harbo jirgin ne da wani makami mai linzami kirar Rasha.

https://p.dw.com/p/1GnKq
Niederlande Präsentation Abschlussbericht Abschuss MH17
Hoto: Getty Images/AFP/E. Dunand

Sakamakon da masu bincike kan musabbabbin faduwar jirgin Malesiya a cikin watan Yulin shekarar bara a gabashin Ukraine suka bayyana ya nunar da cewa jirgin ya fadi ne a sakamakon harbinsa da aka yi da wani makami mai linzami kirar kasar Rasha.

Cibiyar kasar Holland wacce ta gudanar da binciken ta bayyana wannan sakamako nata ne a wannan Talata inda ko da ya ke ba ta fito fili karara ta bayyana wanda ya harba makamin takamaimai ba, amma ta ce an harbe shi ne daga yankin gabashin kasar ta Ukraine da ke a hannun 'yan tawayen kasar masu samun goyan bayan kasar Rasha.

Tuni dai hukumomin kasar Rasha suka yi watsi da wannan sakamakon binciken wanda hukumomin kasar ta Ukraine suka bayyana gamsuwarsu da shi. A ranar 17 ga watan Julin shekara ta 2014 ne dai wani makami ya harbo jirgin na Malaisiya mai lambar tashi MH 17 dauke da mutane 298 kuma babu mutun daya da ya tsira daga cikinsa.