An kwaso 'yan gudun hijira daga Libiya zuwa Nijar
April 19, 2019Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kwashe 'yan gudun hijira 163 daga kasar Libiya zuwa kasar Nijar a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki a kasar inda majalisar ta ce yanzu haka akwai 'yan gudun hijira sama da dubu uku da yakin ya ritsa da su a cibiyoyi dabam-dabam da ake tsare da su a kasar ta Libiya.
A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya Filippo Grandi ya fitar, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin tsira da rayukan 'yan gudun hijirar da rayuwarsu ke cikin hadari.
Wannan shi ne karo na farko da aka kwashe 'yan gudun hijira a kasar tun bayan da sojojin Marshal Khalifa Haftar suka kaddamar da farmakin neman kwace birnin Tripoli daga hannun gwamnatin Fayez Al-Sarraj makonni biyu da suka gabata.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa mutane sama da 200 ne suka mutu wasu sama da 900 suka jikkata a yayin da wasu sama da dubu 25 suka tsere daga gidajensu tun bayan soma wannan yaki.