1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da kasar Libiya ta fada ya dauki hankalin MDD

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
April 6, 2019

Kwamitin Sulhu na Majlisar Dinkin Duniya ya yi kira ga sojojin da ke biyayya ga Khalifa Haftar da su dakatar da dannawar da suke zuwa birnin Tripoli.

https://p.dw.com/p/3GOZI
Libyen Militärische Entwicklungen in Tripolis (Stills aus Reuters TV)
Hoto: Reuters

A wani taron gaggawa na sirri da Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar, kwamitin ya ce yunkurin sojojin da ke yiwa Khalifa Haftar biyayya na karbe iko da birnin Tripoli na zaman wata babbar barazana ga kwarya-kwaryar zaman lafiyar kasar Libiya.

Jakadan Jamus a Kwamitin Sulhu na Majalisr Dinkin Duniya Christoph Heusgen da ya karanto sanarwar bayan taron ya ce kwamitin na sulhu ya bukaci dakatar da duk wani mataki na soja da bangarorin kasar ke dauka, yana mai cewa matakin karfin sojan ba zai kawo wata masalaha ba ga halin da kasar take ciki, kana zai iya gurbata duk wani yunkuri na shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne sosojin da ke biyayya ga Khalifa Haftar da ke rike da gabascin kasar ta Libiya suka yunkuro a anniyarsu ta karbar babban birnin kasar ga gwamnatin hadin kan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.