Majalisar dattijan Amirka ta amince da fadada shingen kan iyaka da Mexico
September 30, 2006Majalisar dattijan Amirka ta amince da kasafin dala miliyan 70 a matsayin kudaden da aka ware na aikin gaggawa ga sojojin Amirka a Iraqi da Afghanistan. Hakan ya sa kasafin da aka warewa ma´aikatar tsaron Amirka a badi zuwa dala miliyan dubu 450. Dukkan wakilan jam´iyun democrats da republicans da yanzu suka dukufa wajen yakin neman zaben ý an majalisun dokoki da za´a yi cikin watan nuwamba, sun kada kuri´ar amincewa da wannan kari, bayan da majalisar wakilai ta amince da wannan mataki tun da farko. A wani labarin kuma majalisar dattijan ta Amirka ta amince da da wani shirin fadada shingen kan iyakar Amirka da Mexico, a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure dake shiga Amirka. Fadada shinge da kilomita kusan dubu 1 zai kara tsawon sa da kashi daya cikin uku a iyakar kasashen biyu mai tsawon kimanin kilomita dubu 10.