1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Amirka ta bijire wa Trump

January 4, 2019

'Yan jam'iyyar Democrats a majalisar Amirka sun sake bude harkokin gwamnati tare da kin amince wa samar da kudade ga Shugaba Trump.

https://p.dw.com/p/3B1Mg
USA Washington - 116 Kongresssitzung: Nancy Pelosi
Hoto: Reuters/K. Lamarque

A wani zaman da suka yi a ranar Alhamis, 'yan jam'iyyar Democrats a majalisar wakilan Amirka sun gabatar da kudurorin sake bude harkokin gwamnatin kasar.

'Yan majalisar sun kuma ki amince wa samar da dala biliyan biyar da Shugaba Donald Trump ke bukata na gina ganuwa tsakanin kasar da Mexico.

Hakan na zuwa ne jim kadan da zabar Nancy Pelosi, mace ta farko a matsayin sabuwar shugabar majalisar.

Kudurori shida ne dai zaman ya amince da su, wadanda za su dauki nauyin al'amuran gwamnati a wannan shekara.

Akwai ma wani da ya shafi kudaden da ma'aikatar harkokin tsaron cikin gida za ta yi amfani da su a Amirkar a bana.

Sai dai fa 'yan jam'iyyar Republican na Shugaba Donald Trump, wadanda ke da karfi a majalisar, na cewa ba za su yi duk wani kudurin da ya saba da ra'ayin shugaban ba.