1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri ta wayi gari cikin alhini

May 5, 2012

'Yan bindigar Boko Haram sun hallaka mutane uku a Maiduguri babban birnin jihar Bornon Najeriya

https://p.dw.com/p/14qeU
The Nigerian military has destroyed the headquarters of the radical Islamist sect Boko Haram that has spread violence across the country?s northern states on July 30, 2009 in Maiduguri, Nigeria. At least 700 people were killed during the confrontation between the security forces and the militia men. (Photo Panapress) +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/ dpa

Wasu mutane dauke da manyan bindigogi sun yi harbe-harbe wajen wani bikin aure a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya inda su ka hallaka mutane uku har lahira. Mutanen dai sun yi harbi irin na kan mai uwa da wabi yayin da su ka fuskanci rundunar tsaro ta hadin gwiwa wato JTF da ta killace wajen bikin.

Da ya ke wa manema labarai karin haske game da faruwar lamarin, kakakin rundunar tsaron ta JTF Lutanant Kanar Sagir Musa ya bayyana cewar wasu 'yan kungiyar nan ta Boko Haram kuma ake nema ruwa a jallo ne su ka shiga garin na Maiduri da nufin hallartar bikin wanda ake zaton na wani dan kungiyar ne -abin da ya sanya jami'an tsaro yi wa wajen tsike. Rundunar dai ta ce ta samu nasarar damke daya daga cikin maharban tare da kame wata mota da ke dauke da bindigogi da albarusai.

Jihar Borno dai ta sha fama da hare-hare a 'yan shekarun nan domin ko a jiya ma sai da wasu mahara su ka kai farmaki a wani gidan yari a garin Kumshe a jihar inda su ka saki ilahirin fursunonin da ke ciki kuma su ka hallaka gandirobobi biyu kamar dai yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Borno Samuel Tizhe ya bayyana wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas