Maiduguri: Harin bam ya kashe mutane 8
October 12, 2016Talla
Wanda suka shaida lamarin sun gayawa DW cewar mata ne guda biyu suka tada bam din a tashar Muna a daidai lokacin da ake jiran jami'an tsaro domin jagorantar matafiya zuwa Dikwa da Gamboru da misalin karfe 8:45 na safe. Wani mazaunin birinin na Maiduguri Mustapha Babagana ya ce lokacin da harin ya auku sun kwashi gawawaki 6 da kuma karin wasu mutane da suka jikkata don kaisu asibiti domin yi musu magani. Mutumin ya ce wasu daga cikin wanda suka jikkata din na cikin mawuyacin hali. Wannan dai shi ne karon farko a cikin watanni da dama da aka samu tashin bam a Maiduguri wadda a baya ya sha fama da tada kayar bayan mayakan Boko Haram.