Maiduguri: Asibitin tafi da gidanka na ICRC
November 5, 2024Iftila'in amabliyar ruwa da aka yi a Maiduguri ya haifar da barkewar cutattuka da ke barazana ga rayuka al'umma musamman saboda karancin cibiyoyin lafiya da ake da su wadan ambaliyar ruwan ta lalata.
Ambaliyar ruwan da aka yi a Maiduguri ya dakatar da ayyukan asibitocin sama da 60 mallakar gwamnati da na ‘yan kasuwa kuma ba dukkaninsu ba ne suka dawo abin da ya sa mutane ke fama da karancin wurare duba lafiya.
Karin Bayani: Maiduguri: Kalubalen harkokin lafiya bayan ambaliya
A birnin Maiduguri musamman wadanda ambaliyar ta shafa da yawancinsu suka rasa gidajensu suna cikin wadanda suke fuskantar kamuwa da cutattuka da ke barazana ga rayuwarsu.
Bisa wannan ne kungiyar ICRC ta fito da wasu cibiyoyin lafiya na tafi da gidanka don taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa da suka kamu da cutattuka.
Malama Hannatu Kachalla wata jami'ar lafiya ce da ke aiki da Kungiyar ta ICRC ta yi min bayanin irin cututtukan da suke samu tattare da mutanen da kuma matakin da suka dauka na taimaka musu.
Karin Bayani: Birnin Maiduguri ya fuskanci ambaliyar ruwa
"Muna bada magunguna ga marasa lafiya yara da manya gaba daya, duk wanda ya zo mana da damuwa idan har muna da magani zamu bashi. Mun yi Goni Kacahallari yanzu kuma muna Simari. Muna kira ga al'umma su fito a basu magunguna saboda gaskiya suna fama da zazzabin Malaria da Gudawa sosai. gaskiya kuma suna zuwa sosai muna samun marassa lafiya sosai.”
Wasu daga ciki wadanda iftila'in ambaiyar ruwan ya shafa suka da samu taimakon lafiya sun bayyana abubuwan da ke damun su da ma yadda suka ji da wannan tallafi.
Masana da masharhanta kamar Badiya Sani Ya'u na ganin taimakon ya zo a kan gaba don abin da mutane suke da bukata ne a ka yi musu.