Mai yiwuwa Girka ta lashe amanta
July 28, 2012Ƙungiyoyin bada rancen ƙasa da ƙasa sun faɗawa Frime Ministan Girka Antonis Samaras cewa bashi da wani zaɓi da ya wuce aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun da zasu samar da irin sauye-sauyen da ƙasar ke buƙata, idan har ƙasarsa na so ta cigaba da samun tallafi.
Daga farkon wannan makon ne masu bincike na ƙasa da ƙasa daga ƙungiyar Tarayyar Turai da Asusun bada Lamuni na Duniya wato IMF da babban bankin Turai suka isa Girka domin gudanr da bincike kan sahihancin shirye-shiryen da Girkar ta tanada wajen daƙile matsalar kuɗinta da ya shiga wani hali na haula'i.
Samaras wanda gwamnatin haɗakarsa ta fara aiki a watan da ya gabata, na fuskantar matsin lamba daga ɓangarorin da ke baiwa ƙasar tallafi, na cewa ya yi aiki da matakan tsuke bakin aljihun da aka gabatarwa Girkar tun farko ko kuma ya rasa kuɗaɗen da ke taimakawa ƙasar a halin yanzu tana gudanar da abubuwan da suka wajaba a kanta.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi