MAHAWARA KAN SABON KUNDUN TSARIN MULKIN ZAMBIYA.
September 15, 2004Cikin shekaru 40 na samun yancin kann Zambia,an sauya kundun tsarin mulkin kasar sau 3,a yanzu haka kuma ana shirin shiga muhawara kann wani sabon kundun tsarin mulki,batu daya kawo sabani tsakanin magabata da Alummar kasar.
A karshen makon daya gabata ne shugaba Levy Mwanawasa na Zanbia ya sanar dacewa zaa jinkirta batun sabon kundun tsarin mulkin har zuwa shekarata 2008,ayayinda kungiyoyi da wakilan alumma da suka halarci taron tattauna kundun tsarin mulkin ke muradin kaddamar dashi kafin zaben kasa baki daya, dazai gudana a shekarata 2006,domin tabbatar da adalcin wannan zabe.Kungiyoyin dai na fatan ayi amfani da wasu shawarwari dake gaban hukumar sake nazarin kundun,komitin data fara aikin tun a watan mayun shekarar data gabata.
Daga cikin shawarwarin dai ,akwai bukatar dan takaran shugabancin Zambia ya samu kashi 51 daga cikin 100 na yawan kuriu da zaa kada lokacin zaben.Shugaba Mwanawasa,ya haye ragamar shugabancin wannan kasa a zaben daya samu kashi 28 daga cikin 100 na yawan kuriu da aka kada a shekara ta 2002,ayayinda mai biye masa da yawan kuriu a zaben Anderson Mazoka,ya samu kashi 26 daga cikin 100.
Bugu da kari,bisa ga sabon tsarin akwai bukatar kowane dan takaran shugaban kasa ya samu nasara a sama da gunduwowi biyar daga cikin 9 dake wannan kasa,wanda zai tabbatar da irin goyon bayan dayake dashi tsakanin alummar kasar,ayayinda bazaa rantsar da dashi ba sai an kammala dukkan batutuwan zargi dangane da magudi da wasu koke koke a gaban kuliya.
A zaben daya bawa shugaban na yanzu nasara dai,uku daga cikin abokan takararsa sun zargi magudi,tare da amfani da kudaden gwamnatin Zambia wajen gudanar da campaign,batutuwa da suka sabawa dokokin zabe a wannan kasa.
An maye gurbin Kundun tsarin Mulki da Zambian ta samu bayan samun yancin kai daga Britania a shekarata 1964,a shekarata 1973,akarkashin shugaba Kennet Kauda,wanda yayi amfani da kundun wajen mayar da kasar a karkashin jammiya guda.A shekarata 1991 aka sake kundun tsarin mulkin ,inda aka maido da Zambia kasa mai jammiyu masu yawa,ayayinda aka sake kundun a shekarata 1996,inda aka kayyade lokacin da kowane shugaba zai kasance akan karagar mulki.A wancan lokacin anyi watsi da batun kowane dantakara ya samu kashi 51 daga cikin 100 na yawan kuriu da aka kada kafin ya samu nasaran zabe,kamar yadda akayiwa batun bawa kowane Dan asalin Zambiyan daman yin takara ba tare da laakari da inda iyayensa suka fito ba.A karkashin kundun tasarin mulkin na yanzu dai,dole ne iyayen kowane dan takara su kasance haifaffun kasar ta Zambia.
A dangane da wadannan batutuwa ,kungiyoyi masu zaman kansu da wakilan alumma ke bukatar majalisar kasar su amince da sabon kundun tsarin mulkin,wanda zai bawa kowane bangare daman tofa albarkacin bakinsu.Bugu da kari sun kuma bukaci gudanar taron kasa,domin tattauna sabon kundun tsarin mulkin.
To sai dai gawamnatin Zambian na adawa dayin hakan,domin hakan injita zai bukaci kashe kudade masu yawan gaske,a wannan kasa da kashi 64 daga ciki 100 na alummarta ke rayuwa akan kudi kasa da dala guda a kowane yini.
Zainab A.Mohammed.